8 Maris 2022 - 15:48
Faransa Ta Sanar Da Hallaka Wani Jigon Al-Qaida A Mali

Rundinar sojin Faransa, ta sanar da kashe wani shugaban mayakan dake ikirari da sunan jihadi a Mali.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Sanawar ta ce an hallaka Yahia Djouadi, dan asalin kasar Aljeriya, da ake wa lakabi da Abou Ammar al-Jazairi, wanda kuma igo ne mai tarihi a kungiyar al-Qaïda a yankin Maghreb a cikin daren ranar 25 zuwa 26 ga watan Fabarairu da ya gabata a kimanin kilomita 100 daga arewacin Tumbuktu.

Faransa ta ce sojojin na ta sun so cafke Yahia Djouadi, saidai turjiyar da ya nuna ta sa aka kai ga hallaka shi.

Al-Jazairi, ya kasance na hannun daman shugaban kungiyar Aqmi, Abdelmalek Droukdel, wanda shi ma sojojin faransa suka hallaka a ranar 3 ga wtan Yunin 2020.

A shekarar 2015, Al-Jazairi, ya kasance shugaba Aqmi a LIbiya, kafin daga bisani ya bulla arewacin Tumbuktu a 2019, a matsayin mai kula da harkokin kudi da kayayakin gungun kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Ya kuma taka mahhiyar rawa wayen wanzuwar ayyukan ta’addanci a yammacin Afrika, wannan ya sa ake ganin mutuwar tasa babban koma baya ne ga kungiyoyin masu ikirarin jihadi a yankin.

342/